Daga Nana Aisha Uwar mu'minai tace::

1. Daga Nana Aisha Uwar Mu'minai (رضي الله عنها), ta ce: "Manzon Allah ﷺ ya Kasance idan ya ga abinda ransa yake so sai ya ce: *Alhamdulillahi-llazee bini'matihi tatimmu-ssalihaat,* idan kuma ya ga abinda ransa ba ya so, sai ya ce: *Alhamdulillahi Ala Kulli Haal."* _Ibn Mājah_. 2. Manzon Allah ﷺ ya ce: *" Duk bawan da yake karanta wannan addua safe da yammaci, kullun, sau uku, babu wani abu da zai cutar da shi, adduar ita ce : (( Bismillahillazee La ya dhurru maa ismihee shaiun fil ardhi wa la fissama'i wa huwassamiul Aleem. )) Abu dawud da Tirmizi. 3.Manzon Allah ﷺ ya ce: *"Idan kuka ji carar zakara toh ku roƙi Allah daga cikin falalarsa* (sai ku ce: *ALLAHUMMA INNEE AS'ALUKA MIN FADLIKA); domin Mala'ika ya gani, idan kuma kuka ji kukan jaki toh ku nemi tsarin Allah daga Sheɗan;* (sai ku ce: *A'UZU BILLAHI MINASSHAITHAANI - RRAJEEM) domin lallai sheɗani ya gani."* _Imamul Bukhari da Muslim_

Comments