Daga Nana Aisha Uwar mu'minai tace::
1. Daga Nana Aisha Uwar Mu'minai (رضي الله عنها), ta ce:
"Manzon Allah ﷺ ya Kasance idan ya ga abinda ransa yake so sai ya ce: *Alhamdulillahi-llazee bini'matihi tatimmu-ssalihaat,* idan kuma ya ga abinda ransa ba ya so, sai ya ce: *Alhamdulillahi Ala Kulli Haal."*
_Ibn Mājah_. 2. Manzon Allah ﷺ ya ce:
*" Duk bawan da yake karanta wannan addua safe da yammaci, kullun, sau uku, babu wani abu da zai cutar da shi, adduar ita ce :
(( Bismillahillazee La ya dhurru maa ismihee shaiun fil ardhi wa la fissama'i wa huwassamiul Aleem. ))
Abu dawud da Tirmizi.
3.Manzon Allah ﷺ ya ce:
*"Idan kuka ji carar zakara toh ku roƙi Allah daga cikin falalarsa* (sai ku ce: *ALLAHUMMA INNEE AS'ALUKA MIN FADLIKA); domin Mala'ika ya gani, idan kuma kuka ji kukan jaki toh ku nemi tsarin Allah daga Sheɗan;* (sai ku ce: *A'UZU BILLAHI MINASSHAITHAANI - RRAJEEM) domin lallai sheɗani ya gani."*
_Imamul Bukhari da Muslim_
Comments
Post a Comment